Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Sahara Reporters cewa, an gudanar da muzaharar ta Arbaeen Hussaini a titunan garin Kaduna Najeriya, tare da halartar daruruwan masoya Imam Hussaini (AS) da dimbin mabiya addinin musulunci da (IMN) ta shirya.
Wasu rahotanni sun bayyana cewa, a ranar Litinin din da ta gabata a Zariya, jami’an ‘yan sanda da ga dukkan alamu sun yi wa ‘yan kungiyar IMN kwanton bauna, sun harba harsasai masu rai da hayaki mai sa hawaye don tarwatsa masu zanga-zangar ta Arbaeen, inda suka jikkata da dama daga cikinsu.
Wannan dai ba shi ne karon farko da ‘yan sanda ke kai wa ‘yan kungiyar IMN hari ba a lokacin da suke gudanar da zanga-zangar, Jami’an ‘yan sanda sun yi ta harbe-harbe da su a ‘yan watannin nan.
Ko a lokacin gudanar da wani jerin gwano a lokacin Ashura an samu irin wannan, inda jami’an tsaro suka auka wa masu jerin gwanon, lamarin da ya yi sanadiyyar rasa rayuka da kuma jikkatar mutane.