IQNA

Shiri Na Musamman Na Karatun Kur'ani Da Ya Kebanci Mata A Hubbaren Imam Ali (AS)

22:02 - November 01, 2021
Lambar Labari: 3486500
Tehran (IQNA) Cibiyar kur'ani mai tsarki da ke karkashin hubbaren Imam Ali (AS) ta kaddamar da kwas na koyon karatun kur'ani ga mata.

Cibiyar kur'ani mai tsarki da ke karkashin kulawar hubbaren Imam Ali (AS) ta kaddamar da kwas na hudu na koyon  sauti na karatun kur’ani wanda ya kebanci mata zalla.

Rasha Al-Tarfi mataimakiyar shugabar kungiyar mata ta Darul-Qur'ani mai alaka da wannan cibiya ta bayyana cewa, za a gudanar da kwas din na tsawon watanni 3, zama 2 a mako.

Ta ce  kuma kwamiti na musamman na wannan cibiya ya amince da karatun share fage.

Cibiyar Alqur'ani, ta sanar da cewa ya zuwa yanzu 360 daga cikin wadannan mata an rabasu zuwa rukunoni kungiyoyi daban-daban.

Al-Tarfi ta ci gaba da cewa; An fara gudanar da wannan kwas ne da taron kur'ani mai tsarki wanda aka samu halartar mata, kuma bayan karanta ayoyin kur'ani mai tsarki da kuma tawashih na kur'ani, da bayanin yadda ake gudanar da kwasa-kwasan da kuma hanyoyin ilmantarwa da gudanarwa ga matan kur'ani.

 

4009596

 

 

captcha