IQNA

Amurka Na Shirin Rufe Kurkukun Tsibirin Guantanamo

20:00 - May 03, 2021
Lambar Labari: 3485874
Gwamnatin Amurka ta fara yin nazari kan rufe kurkukun nan da ta gina a tsibirin Guantanamo na kasar Cuba.

Tashar RT ta bayar da rahoton cewa, sakataren harkokin wajen kasar Amurka Antony Blinken ya bayyana cewa, suna da niyyar rufe kurkukun Guantanamo nan da wasu ‘yan watanni masu zuwa.

A wata zantawa da ya yi da tashar CBS ta kasar Amurka, Antony Bliken ya bayyana cewa, ci gaba da wanzuwar kurkukun Guantanamo ba ta da wani amfani, saboda hakan shugaban kasar Amurka Joe Biden yana da niyyar rufe shi.

Tun a cikin shekara ta 2002 ce dai tsohon shugaban kasar Amurka George W. Bush ya bude wannan kurkuku, inda aka fara tsare wasu mayakan kungiyar Taliban su 20, bisa zarginsu da hannua  harin 11 ga watan Satumba.

Daga bisani Amurka ta ci gaba da kai daruruwan mutane a wurin, akasarinsu ‘yan kungiyar aka’ida ne da kuma ‘yan Taliban, kuma da dama daga cikinsu sun fito ne daga Saudiyya, Afghanistan da kuma Yemen.

Sakamakon yadda aka yi ta samun bayanai kan yadda sojojin Amurka suke azabtar da wadada suke tsare da su a  wurin, a cikin watan Janairun 2009 shugaban kasar Amurka na lokacin ya bayar da umarnin rufe wannan kurkuku, amma majalisar dokokin Amurka ta fitar da kudiri wanda ya hana aiwatar da umarnin na Obama, wanda hakan yasa wurin ya ci gaba da kasance a bude har zuwa yau.

 

3968866

 

 

 

captcha