Shaffin yada labarai na businessnews.com ya bayar da rahoton cewa, Shekh Usman Battikh babban malami mai bayar da fatawa na kasar Tunisia ya bayyana cewa, batun azumi a cikin lokacin da ake fama da corona, na bukatar nazarin masana kiwon lafiya.
Y ace a halin yanzu ba zai iya bayar da fatawa ba kan batun ba tare da yin shawara da kuma jin mahangar likitoci kan wannan lamari ba.
Ya kara da cewa, a zaman da za a yi gobe zai yanke matsaya bayan jin ta bakin masana kan harkokin lafiya, dangane da yadda tasirin corona yake ga mutane masu azumi.