Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin Alwatan News cewa, ma’aikatar kula da harkokin addinia kasar Masar ta sanar da cewa an sakawa gasar kur’ani ta duniya a Masar sunan Abdulbasit Abdulsamad, sakamakon irin gagarumar hidimar da marigayin ya bayar a duniya wajen hidima ga alkur’ani mai tsarki, wanda za a gudanar da gasar karo na ashirin da bakawai ne a cikin watan Fabrairun 2020.
Shugaban kasar Masar abdulfattah Sisi ne da kansa zai girmama wadanda suka nuna kwazo a gasar a daren 27 ga watan Ramadan mai zuwa.