Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, wani mutum dan kasar Auzbakistan mazaunin birnin Bukhara, ya tafi da wannan kwafin kur’ani zuwa birnin Fargana domin sayar da shi a kan farashin kudi dalar Amurka dubu 200, amma jami’an tsaro sun kama shi.
Wannan kur’ani dai an rubuta shi ne tun a cikin karni na 16 kimanin shekaru dari biyar da suka gabata, wanda Mukka yusuf Sakhaf wani mai fasahar rubutu ya rubuta.
Ana ajiye da wannan kwafin kur’ani ne a dakin ajiye kayan tarihi na garin Sarmakand, kuma a cikin karni na 19 ne aka sake gyara tsarin wannan kwafin kur’ani.