IQNA

Taron Karawa Juna Sani Na Addinai A Jami'ar Azhar

16:15 - January 10, 2018
Lambar Labari: 3482285
Bangaren kasa da kasa, a yau ne ake bude taron karawa juna sani na mabiya addinai da aka saukar daga sama a jami'ar Azhar.

Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Misri Alyaum cewa, an fara taron karawa juna sani na mabiya addinai da aka saukar daga sama a babban ginin jami'ar Azhar da ke birnin Alkahira fadar mulkin kasar masar.

Wannan taro yana guda ne bisa daukar nauyin ma'aikatar kula da harkokin wasannan da matasa da kuma cibiyar ta Azhar.

Daga cikin mahalrta wurin akwai malamai na mabiya addinan muslunci da kiristanci, da kuma masana daga dukkanin bangarorin biyu, haka nan kuma akwai wasu daga cikin jami'an gwamnati da suke halartar wurin.

Babbar manufar gudanar da wannan zaman taron dai ita ce samar da wani yanayi na wayar da kan mabiya dukkanin addinai da aka saukar daga sama, kan cewa dukkanin wadannan addinai suna kira zuwa ga zaman lafiya ne.

Wannan kuwa yana zuwa ne sakamakon karuwar kungiyoyin 'yan ta'adda da ake samu da sunan addini, wadanda zubar da jinin bil adama da sunan suna yin aikin addini, kamar yadda ita kanta kasar ta Masar bata sha ba dangane da irin wadannan ayyuka.

3680725

 

captcha