IQNA

Hotunan Kur’ani Da Aka Kammala Gyaransa A Masar

21:54 - August 20, 2017
Lambar Labari: 3481815
Bangaren kasa da kasa, a yau an gudanar da taron muka kwafin kur’ani mai tsarki na tarihi wanda aka kammala a gyaransa a kasar Masar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, ya nakalto daga shafin yada labari na Misr Al-arabiyyah cewa, wannan kur’ani mai suna kur’anin Usaman an kwashe tsawon shekaru 133 ana ta kokarin yi masa gyara.

An nuna kwafin kur’ani a yau a babbar cibiyar adana kayan tarihi ta Qustat da ke kasar ta Masar, tare da halartar manyan mutane da suka hada da jami’an gwamnati da kuma malamai gami da masana na ciki da kuma wajen kasar.

Ana danganta wannan kwafin kur'ani da lokacin mulkin Khalifa Usaman dan Affan wato khalifa na uku, inda ake bayyana cewa yana daga cikin kur'anan da ya bayar da umarni a rubuta a birane na musluncia wancan lokacin, amma dai ana gudanar da bincike domin tabbatar da hakan.

An ce rubutunsa yana kowa zuwa ga shekara ta 25 bayan hijirar manzon Allah ne, mata 7 ne kwararru kan gyaran kayan tarihi tare da wani kwarren dan kasar Amurka ne suka gudanar da wannan aiki da ya dauki tsawon shekaru shida.

3632558


captcha