IQNA

Hojjatol Islam Jarari: Marigayi Imam Khomeini Ya Bayar Da Gudunmawa Domin Hada Kan Musulmi

14:47 - February 03, 2021
Lambar Labari: 3485616
Tehran (IQNA) Daga cikin muhimman ayyukan da marigayi Imam Khomeni ya gudanar a lokacin rayuwarsa har da kokarinsa na ganin an samu hadin kai tsakanin musulmi.

A ci gaba da  gudanar da tarukan tunawa da zagayowar ranakun samun nasarar juyin juya halin musulunci a kasar Iran, ana gabatar da jawabai a taruka daban-daban da ake gudanarwa.

A cikin bayanin da daya daga cikin malamai ya gabatar a irin wadannan taruka da ake gudanarwa a birnin Tehran, Hojjatol Islam Jarari ya bayyana cewa, daya daga cikin muhimman ayyukan da marigayi Imam Khomeni ya gudanar a lokacin rayuwarsa shi ne kokarinsa na ganin an samu hadin kai tsakanin musulmi.

Malamin ya ce' wannan yunkuri na marigayi Imam yana da babban tasiri wajen farkar masu zurfin tunani daga cikin mususulmi wajen fadaka daga kuma gane cewa, dukkanin matsalolin da musulmi suke fuskanta a halin yanzu a duniya, babban tushen hakan shi ne rashin hadin kan da ke tsakaninsu.

A lokacin da yake raye da dama daga cikin musulmi ba su fahimci hakan ba, amma manyan masu kiyayya da musulunci a musulmi a duniya sun fahimi hakan sarai, cewa idan musulmi suka hada kansu a duniya, to babu wanda ya isa ya nuna musu yatsa.

Wannan ya sanya manyan kasashe masu adawa da musulunci sun kara kaimi matuka wajen fada da wannan tunani na marigayi Imam Khomeini, tare da kokarin yin amfani da dukkanin hanyoyin da za su iya wajen ganin sun kange musulmi daga abin da yake kokarin nuna musu.

Malamin ya ci gaba da bayani da cewa, abin ban takaici shi ne yadda makiya musulunci suka hada kai da wasu daga cikin manyan kasashen musulmi masu magana da yawun musulunci, domin cutar da musulunci da kuma kasashen musulmin.

Inda  ya ce a halin yanzu a duk inda ake yakar wata kasar musulmi to tabbas wasu daga cikin manyan kasashen musulmi ne kan gaba a wannan yakin a kan musulmi, ba don komai ba, sai domin su burge manyan kasashen duniya irin su Amurka, da kuma yahudawa, a lokaci guda kuma suna yin amfani da irin malaman da suka samar, domin kara fadada baraka da rashin jituwa a tsakanin musulmi, wanda shi ne abin da yake faruwa a halin yanzu a duniyar musulmi.

Malamin ya ce amma duk da haka, masu zurfin hankali da hangen nesa daga cikin musulmi sun iya gano cewa wannan makirci ne na makiya musulunci, kuma sannu a hankali shamaki na ci gaba da yaye wa ga masu idon basira daga cikin musulmi.

 

3951608

 

 

 

 

 

captcha