IQNA

Gwamnatin Iran Ta Kirayi Jakadan Faransa A Kan Batun Batunci Ga Manzon Allah (SAW)

22:54 - October 27, 2020
Lambar Labari: 3485309
Tehran (IQNA) ma’aiktar harkokin wajen kasar Iran ta kirayi jakadan kasar Faransa da ke Tehran, domin mika masa sako na bacin rai dangane da cin zarafin manzon Allah (SAW) a kasar Faransa.

Ma’ikatar harkokin wajen kasar ta Iran ta sanar da cewa, ta kirayi jakadan na faransa ne domin mika masa sako zuwa ga gwamnatin Faransa, da ke dauke da nuna rashin amincewa da cin mutuncin manzon Allah da ake yi a kasar ta Faransa.

Sakon ya yi ishara da cewa, keta alfarmar manzon Allah (SAW) da cin zarafinsa, na a matsayin keta alfarma da cin zarafin dukkanin musulmi kusan biliayn biyu da suke rayuwa  a duniya.

Daga karshe bayanin na gwamnatin Iran ya bukaci gwamnatin Faransa da ta gaggauta daukar dukkanin matakai na dakatar da duk wani nau’in batunci da cin zarafi da kuma keta alfarmar ababe masu tsarki na addinin muslunci a cikin kasarta, musamman wanda ya shafi madaukakin matsayi na manzon Allah (SAW) wanda ba abu ne da msuulmi za su iya jure masa ba.

Jakadan kasar Faransa a Tehran ya yi alkawalin mika wannan sako na gwamnatin Iran ga gwamnatin Faransa cikin gaggawa.

3931465

 

 

 

captcha