IQNA

An Yi Allawadai Da Kalaman Tozarci Da Tsohon Jami’in Gwamnatin Saudiyya Ya Yi Kan Falastinawa

23:18 - October 10, 2020
Lambar Labari: 3485263
Tehran (IQNA) kungiyoyin Hamas PLO sun yi Allawadai da kalaman cin zarafi da tsohon jami’in gwamnatin Saudiyya ya yi kan falastinawa.

Kafofin yada labarn Falastinu sun bayar da rahoton cewa, kungiyar Hamas tare da kungiyar kwatar ‘yancin kan Falastinawa ta PLO sun yi Allawadai da kalaman cin zarafi da tsohon jami’in shugaban hukumar leken asirin kasar Saudiyya Bandar Bin Sultan ya yi kan falastinawa.

Kakakin kungiyar Hamas Sami Abu Zahri ya bayyana cewa, kamalan na Bandar Bin Sultan tozarci ne ga dukkanin al’ummar Falastinu, kuma abin yin tir da Allawadai ne da su.

Shi ma a nasa bangaren Sa’ib Uraikat daya daga cikin manyan kusoshi na Fatah ya bayyana furucin na Bandar da cewa ba a abu ne da Falastinawa za su lamunta da shi ba.

A wata zantawarsa da tashar Alarabiyya mallakin gwamnatin Saudiyya da ke watsa shirinta daga birnin Dubai, Bandar Bin Sultan ya ci zarafin Falastinawa, da kuma kalamai na batunci a kansu, saboda sun ki amincewa da matakin da Bahrain da UAE suka dauka na kulla alaka da yahudawan Isra’ila, inda ya bayyana su da kidahumai.

 

3928343

 

 

captcha