IQNA

Amurka:Taron Buda Baki Mai Taken “Ba Ma Son Buda Bakin Trump”

22:44 - June 07, 2018
Lambar Labari: 3482737
Bangaren kasa da kasa, babbar kungiyar musulmi ta kasar Amurka ta shirya wani buda baki a yammacin jiya a gaban fadar White House mai take ba ma son buda bakin Trump.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Nahad Iwad shugaban kungiyar musulmin Amurka ne ya jagoranci gudanar da wannan buda baki, a daidai lokacin da Trump ya gayyaci wasu musulmi zuwa buda baki a cikin fadar white house.

Nahad Iwad ya ce kungiyarsu tare da wasu kungiyoyin musulmi ma wasu masu kare hakkin bil adama ne suka shirya buda bakin domin nuna yarda da abin da Trump yake na kyamar musulmi.

Ya ce babu gaskiya a cikin gayyatar da Trump ya yi wa wasu musulmi, domin shi makiyin musulmi ne, babu yadda za a yi ya so musulmi balantana har ya kalli azumins a matsayin wani mai daraja, saboda haka sun san wannan yaudara e kawai.

Tun bayan da Trump ya dare kan kujerar sugabancin Amurka, ya yi watsi da gayyatar da shugabannin Amurka suke yi wa musulmi zuwa buda baki a fadar white house, inda yake kallon hakan a matsayin bata lokaci kawai, amma kuma a jiya kwatsam sai ya kira wasu zuwa buda baki.

3720751

 

 

captcha