IQNA

Wani Dan kasar Holland ya Zama Musulmi

13:53 - September 28, 2017
Lambar Labari: 3481943
Bangaren kasa da kasa, wani dab kasar Holland ya zama sakamakon jin kiran salla a kasar Turkiya a lokacin da yake yawon bude ido.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya ahbarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Aksham cewa, wani dab kasar Holland ya zama sakamakon jin kiran salla a kasar Turkiya a lokacin da yake yawon bude ido a garin Qaisaria.

Bayan ya musluncta ya zabi sunan Muhammad Mustafa a matsayin sabon sunansa na addinin muslunci.

Ya ce a lokacin da ya ji kiran salla jikinsa ya yi sanyi matuka, kuma ya ji wata natsauwa da bait aba jin irinta arayuwarsa sakamakon hakan, wanda wannan ya tabbatar masa da cewa lallai addinin musulunci shi ne gaskiya, domin kuwa a cikinsa natsuwar ruhi take.

Ya ci gaba da cewa, duk da cewa iyayensa mabiya addinin kirista ne, bayan ya muslunta ya sanar da su, kuma babban abin da ya kara faranta masa rai shi ne, iyayensa da sauran danginsa sun mutunta ra'ayinsa da kuma zabinsa.

Dangane da halin da musulmi suke a cikin nahiyar turai kuwa na damuwa kna cin zarafin da ake yi musu, ya bayyana cewa hakikanin gaskiya ya san irin halin da musulmi suke ciki, kuma yana fatan ya zama daga cikin wadanda za su taka rawa wajen tunkarar irin wannan kin jinni da ake nuna ma musulmi a nahiyar turai.

3647586


captcha