IQNA

Taron Maulidin Imam Ridha (AS) A Cibiyar Alkauthar A Holland

21:51 - August 01, 2017
Lambar Labari: 3481756
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da taron maulidin Imam Ridha (AS) a cibiyar Alkauthar da ke birnin Hague a kasar Holland.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na alcauther.com ya bayar labarin cewa, wannan cibiya tana isar da sakon taya murnar zagayowar lokacin haihuwar limamin shiriya na iyalan gidan manzon rahma Imam Ridha (AS) ga Imam hujja Allah ya gaggauta bayyanarsa da sauran al'ummar musulmi.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan taro zai samu halartar malamai da kuma masana gami da sauran muminai, inda za agabatar da jawabai a kan matsayin wannan limami mai tsarki da kuma tarihin rayuwarsa mai albarka.

Daga cikin wadanda za su gabatar da jawabai da kuma bege ga Imam Ridha (AS) akwai sheikh Haidar Arab, da kuma Haji Abu Ali Algiyawi, wadanda dukkaninsu sanannun fuskoki wajen gabatar da irin wadannan jawabai a kan limamai masu tsarki.

Cibiyar ta alkauthar ta ce tana mika gayyata ga dukkanin masu sha'awar halartar wannan taro maza da mata, wanda zai fara daga karfe 19 na daren Juma'a, kuma za akebance wurin mata daban da kuma na maza daban.

3625465


captcha