IQNA

Azahar Ta Yi Suka Dangane Da Nuan Bidiyon Cin Zarafin Ma’aiki A Talabijin Na Holland

23:53 - June 26, 2015
Lambar Labari: 3319698
Bnagaren kasa da kasa, babbar cibiyar muslunci a kasar Masar at Azahar ta yi akkakusar da yin Allawadai dangane da fitar da wani fafan bidiyo na cin zarafin manzon Allah (SAW) a tashar talabijin ta Holland.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Sky News bangaren larabaci cewa, babbar cibiyar muslunci a kasar Masar at Azahar ta yi akkakusar da yin Allawadai dangane da fitar da wani fafan bidiyo na cin zarafin manzon Allah (SAW) a tashar talabijin ta Holland.

Geert Wilders dan majalisar dokokin Holalnd mai kiyayya da muslunci ya fitar da zanen batunci goda 10 na tsawon minitina biyu da sakan 44 wanda aka nuna talashar talabijin ta NOS a kasar, lamarin da ya bakantawa dukkanin musulmin kasar da na duniya baki daya.

Bayanin ya ci agba da cewa babu wani dalili da zai sanya a rika cin zarafin addinin muslucni ta hanyar taba manzon Allah (SAW) da cin zarafinsa, wannan na daga cikin abubuwan da suke kara jawo rashin fahimta tsakanin abiya addinin musulunci da masu yin hakan.

A kowane lokaci musulmi suna son zaman lafiya kuma bas u daukar mataki na nuna kiyayya ga duk wani addini, bil hasali ma su suna gayyatar kowa cikin lamarinsu domin tabbatar da kyawawan dabiu da musulunci ya koyar da su, amma wasu masu tsatsauran ra’ayi suna tsokanar su.

A bangare guda cibiyar ta kiayi mahukunta a kasar da su sake shawara domin barin irin wannan mummunan aiki yana gudana a cikin kasar, baya a nufin fadin albarkacin baki ko bayyana ra’ayi, hakan nuna kiyayya ne ga wata akida da addini na wani babban bagare na mutanen duniya.

3318557

Abubuwan Da Ya Shafa: holland
captcha