Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Yaum Sabi ta kasar Masar cewa, 'yan ta'addan sun tarwatsa masallacin ne baki daya a yau bayan da suka dasa wasu nakiyoyin a cikinsa, kuma suka yi amfani da na'urorin tayar da bama-bamai daga nesa wajen rusa shi, masallacin dai ya kasance daya daga cikin masallatai mafi dadewa a kasar Iraki da aka gina shi tun lokacin tabi'ai.
'Yan ta'addan ISIS dai sun rusa masallatai da wuraren ibada da dama a cikin kasashen Iraki da Syria, da hakan ya hada har da kabrukan annabawa da na sahabbai da sauran bayin Allah, lamarin da malaman addinin muslunci a kasashen daban-daban da suka hada hard a na babbar jami'ar muslunci ta Azahar da ke Masar suka bayyana hakan da cewa ba addinin muslunci ba ne.