IQNA

Al Jazeera ta yi bincike kan;

Martani game da hijabin matar Biden a Masallacin Al-Azhar

19:45 - June 06, 2023
Lambar Labari: 3489262
Tehran (IQNA) A cikin wani rahoto da tashar talabijin ta Aljazeera ta fitar ta bayyana yadda masu amfani da shafukan sada zumunta suka mayar da martani dangane da kasancewar uwargidan shugaban kasar Amurka sanye da hijabi a masallacin Azhar inda ta ambato su na cewa: lamarin ya girgiza kowa da kowa. ... wannan alama ce ta bukatar kiyaye tsarkin wurare masu tsarki, daga kowa ne a kowane matsayi.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Aljazeera cewa, a ranar Juma’ar da ta gabata ne uwargidan shugaban kasar Amurka Jill Biden, a ziyararta a kasar Masar, ta ziyarci Masallacin Azhar.

Daya daga cikin tsare-tsaren da uwargidan shugaban kasar Amurka Joe Biden ta yi a ziyarar da ta kai kasar Masar shi ne ziyartar masallacin Al-Azhar, kuma dangane da haka ta bayyana a harabar manyan masallatai da suka fi shahara da muhimmanci na kasashen musulmi.

A cewar rahoton, Jill Biden ta mutunta al'adun Musulunci sosai a lokacin da ta shiga Masallacin Al-Azhar, ta sanya lullubi a kai sannan ta sa doguwar riga shudiyya sannan ta cire takalmanta sannan ta tafi tare da abokan aikinta suka ziyarci masallacin.

A lokacin da matar Biden ta kai ziyarar gani da ido na dadadden abubuwan tarihi, dandali, dakunan ruwa da kuma ma'adanai na masallacin Al-Azhar, wanda aka gina tun a shekara ta 1083 miladiyya, matar Biden ta saurari bayanin shugaban jami'ar dangane da tarihin masallacin.

Bayan kammala tattakin da ta yi a Masar, uwargidan shugaban kasar Amurka ta raba hotunan ziyarar da ta kai masallacin Al-Azhar a wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter ta kuma mika godiyarta ga jami'an jami'ar Azhar da suka karbe su.

 

4146003

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: masallaci bincike ambato Al-Azhar girgiza
captcha