IQNA

Saudiyya:

Ba zai yiwu a yi aikin Hajji da takardar izinin Umra ba

19:23 - June 05, 2023
Lambar Labari: 3489258
Tehran (IQNA) Ma'aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya ta jaddada cewa ba zai yiwu a yi aikin Hajji da bizar Umra ba.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ma’aikatar aikin hajji da umrah ta kasar Saudiyya ta sanar da cewa, a wannan Lahadin ce rana ta karshe na bayar da izinin umra kafin zuwan aikin hajji.

Ma’aikatar ta kuma jaddada cewa ranar karshe da mahajjata za su tafi Umrah ita ce ranar 18 ga watan Yunin 2023.

A baya ma’aikatar Hajji da Umrah ta kasar Saudiyya ta sanar da cewa, za a iya samun takardar izinin Umrah ta hanyar shirin “Nasq” ko “Tawaklan”, matukar ba a kamu da cutar korona ba, ko kuma a gauraye da masu dauke da cutar.

Saudiyya ta sanar da dalilin daukar wannan mataki na shirya Umrah da kuma kula da cunkoson jama'a a Masallacin Harami.

 

 

4145801

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: hajji jama’a cunkoso umrah mahajjata
captcha