IQNA

Al-Azhar na shirin samar da cibiyar addini a birnin Quds

18:54 - June 05, 2023
Lambar Labari: 3489257
Tehran (IQNA) Jami'ar Al-Azhar ta kasar Masar na shirin kafa wata cibiya ta addini a birnin Kudus da ta mamaye domin tallafawa 'yancin Falasdinawa.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Redna cewa, Ahmad al-Tayeb, shehin Azhar, ya bayar da umarninsa ga jami’an wannan cibiya ta ilimi da addini na kafa wata cibiya a birnin Quds da aka mamaye.

Ahmad al-Tayeb ya jaddada a cikin jawabinsa game da wannan batu cewa, Azhar na ci gaba da tona asirin ayyukan gwamnatin sahyoniyawan a kan al'ummar Palastinu, kuma tana ci gaba da isar da sako ga wannan gwamnatin ta 'yan ta'addar da cewa Azhar za ta tona asirin laifukansu da irin wahalhalun da suke fuskantar Al'ummar Falasdinu.

Ahmad al-Tayeb ya ci gaba da cewa: Azhar za ta ci gaba da yin kira zuwa ga farkar da lamiri na duniya har sai Allah ya kawo karshen wannan aiki na zalunci, wanda ya sabawa dukkan dokokin Ubangiji da na addini.

Ahmad al-Tayeb ya sanar da sha'awar Al-Azhar na karbar karin dalibai daga Falasdinu da kuma fadada tallafin karatu na digiri na biyu a fannin ilimin addinin Musulunci.

Sheikh Azam Al-Azhar ya kuma bayyana nadama da bakin ciki dangane da shirun da kasashen Larabawa da na Musulunci da wadanda ba na Musulunci suka yi ba dangane da batun Palastinu.

 

 

4145872

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: wahalhalu fuskanta falastinu laifuka Al-Azhar
captcha