IQNA

Dakarun Hashd Al-Shaabi Na Iraki Sun Ce A Shirye Suke Su Kai Dauki Ga Al’ummar Falastinu

23:01 - May 16, 2021
Lambar Labari: 3485923
Tehran (IQNA) Dakarun sa kai na al’ummar Iraki sun ce a shirye suke domin kai dauki ga al’ummar Falastinu.

Dakarun sa kai na al’ummar Iraki sun ce a shirye suke domin kai dauki ga al’ummar Falastinu, biyo bayan kiran da Ayatollah Sistani ya yi kan hakan.

A cikin wani bayani da ta ftar a yau, rundunar dakarun sa kai ta kasar Iraki Hashd Al-shaabi ta sanar da cewa, a shirye take ta bayar da dukkanin gundumar da ake bukata wajen taimakon al’ummar Falastinu marasa kariya.

Bayanin ya halin da al’ummar musulmi na Falastinu suke ciki yana tayar da hankali matuka, kuma kamar yadda Ayatollah Sistani ya fada, hakki a kan dukkanin musulmi a ko’ina cikin fadin duniya su taimaka wa  al’ummar Falastinu, kan kisan kiyashin da yahudawan Isra’ila suke yi a kansu.

A cikin kwanaki bakawai da Isra’ila ta kwashe tana luguden wuta  akan yankin zirina Gaza, Falastinawa dari da arba’in ne suka rasa rayukansu, kusan arba’in daga cikinsu kananan yara ne, sai ashirin da biyu mata.

Wannan yana zuwa ne a daidai lokacin da wasu daga cikin gwamnatocin kasashen larabawa suke dora laifin abin da yake faruwa a kan Hamas, ba tare da sun iya yin ko da Allawadai da kisan musulmi da Isra’ila ke yi a Gaza da birnin Quds da sauran yankunan Falastinawa ba.

 

 

3971755

 

captcha