Kamar yadda aka gudanar da sallar idi a shekarar da ta gabata tare da daukar matakai na kiwon lafiya domin hana yaduwar cutar corona, a shekarar bana ma an gudanar da sallar idi a kasashe da dama a cikin irin wannan yanayi.
Tashar Aljazeera ta nuna wasu daga cikin hotuna na yadda aka gudanar da sallar idin karamar salla a yau a kasashen duniya daban-daban.