IQNA

An Yi Jerin Gwanon Nuna Goyon Baya Ga Al'ummar Falastinu A Afirka Ta Kudu

23:25 - May 13, 2021
Lambar Labari: 3485911
Tehran (IQNA) birane daban-daban na duniya, al’ummomi suna gudanar da jerin gwano domin nuan takaicinsu da kisan kiyashin da Isra’ila take yi wa al’ummar Falastinu.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a jiya daruruwan mutane ne suka gudanar da gangami a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta kudu, domin yin tir da Allawadai da kisan kiyashin Isra’ila akan al’ummar Falastinu.

Rahoton ya ce, kungiyoyin musulmi da kuma kungiyoyin kare hakkin bil adama da magoya bayan jam’iyyar socialist ne suka gudanar da wannan gangami, inda suka yi tir da abin da yahudawan Isra’ila suke yin a kisan fararen hula a Gaza da sauran yankunan Falastinawa.

Jami’ai da dama a cikin gwamnatin Afirka ta kudu daga jam’iyya mai mulki da ma sauran jam’iyyu da suke da wakilci a majalisar dokokin kasar, sun yi tir da Allawadai da wannan ta’asa ta Israila akan fararen hula a Falastinu.

A birane daban-daban na kasashen duniya da haka ya hada har da kasashen turai, ana ci gaba da gudanar da irin wannan gangami da jerin gwano, inda ko ajiya laraba, an gudanar da irin wanann gangami a birananen Washington da New York na kasar Amurka, da kuma wasu birane a kasashen Canada, Farasa Jamus Austria da sauransu.

 

3971295

 

 

 

captcha