A rahoton kamfanin dillancin labaran iqna, sakamakon karuwar cutar corona a kasar Jamus Italiya da Faransa, musulmi suna azumi a karkashin dokar zaman gida domin kaucewa yaduwar cutar.
Duk da cewa an sassauta dokar zaman gida a wasu kasashen wadda aka kafa a baya-bayan saboda karuwar yaduwar cutar corona, amma duk da haka a kan kayyade lokuta da mutane da za su iya gudanar da harkokinsu.
A kasar faransa an kafa dokar cewa, dole ne daga karfe 7 na yamma kowa ya koma gida, wanda hakan yasa musulmi ba za su iya gudanar da sallolinsu da suke yi a masallatai ba, kamar yadda suka saba yia kowace shekara, musamman ma sallar asham da ake yi bayan sallar Isha'i a masallatai da dama.
A kasar Italiya kuwa musulmi sun samar da wani tsari ne na taimako, musamman wadanda suke da hali da suke daukar nauyin buda baki a masallatai da cibiyoyin addini, inda suke bayar da taimakon kai tsaye ga mutane domin su yi buda baki a gidajensu.