IQNA

Mohammad Hussain Hassani:

Yada Sulhu Da Zaman Lafiya Da Fahimtar Juna Ita Ce Babbar Manufar Cibiyar Raya Ayyukan Kur’ani Ta Iran

15:10 - March 17, 2021
Lambar Labari: 3485750
Tehran (IQNA) Mohammad Hussain Hassani shugaban cibiyar ayyukan kur’ani ta Iran ya jaddada wajabcin yin aiki domin samun zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin al’ummomin duniya.

A zantawarsa da kamfanin dillancin labaran IQNA, Mohammad Hussain Hassani shugaban cibiyar raya ayyukan kur’ani ta kasar Iran, kuma babban darakta na kamfanin dillancin labaran iqna ya bayyana cewa, yada zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin ‘yan adam ne suka sanya  a gaba.

Ya ce a halin yanzu akwai ayyuka da dama da suke a gaban cibiyar raya ayyukan kur’ani ta kasar Iran, amma mafi muhimmanci daga ciki shi ne yada dukkanin abin da zai kawo zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin al’ummar musulmi, da ma tsakanin sauran al’ummomi na duniya.

Hassani ya ce, daga cikin ayyukan da suke gudanarwa har da shirya tarukan baje koli da suka shafi ayyukan kur’ani a kasashen duniya daban-daban, inda sukan nuna abubuwa da suke da alaka da kur’ani, da suka hada da rubutattun alluna, ko kuma nuna nau’oin kwafin kur’ani.

Baya ga haka kuma akan nuna rubutun kur’ani da aka yi da salo  na fusaha mai kayatarwa, kamar yadda kuma akan saka tarjama ta wasu ayoyi da suke koyar da dana dam abubuwa da suka shafi kyautata zamantakewa, kyawawan halaye, jin kai, tausayi, taimako da dai sauransu.

Dangane da sauran ayyukan kuwa, akwai shirya taruka a manyan dakuna na taruka a kasashe daban-daban, tare da gayyatar malamai daga bangarori daban-daban na mazhabobin muslunci, domin su gabar da jawabai kan irin darussa da suke ciki kur’ani, wadanda yake koyar da musulmi da ma ‘yan adam baki daya.

Ya ce ya zuwa yanzu an samu tasirin hakan, duk kuwa da cewa cutar korona ta kunno kai ta dakatar da abubuwa da dama da suka shafi wannan shiryi, inda a halin yanzu lamurran sun fi takaita a yanar gizo.

Baya ga haka kuma akwai taruka na gasar kur’ani mai tsarki wanda shi ma yana da gagarumin tasiri wajen yada sha’anin kur’ani mai tsarki a duniya, wanda shi ma a wannan karo dukkanin tarukan sun gudana ne ta hanyar hotunan bidiyo na yanar gizo.

3960096

 

 

captcha