IQNA

Falastinawa Sun Yi Maraba Da Matsayar Kungiyar Tarayyar Afirka Ta Nuna Goyon Baya Ga Al’ummar Falastinu

23:53 - February 13, 2021
Lambar Labari: 3485648
Tehran (IQNA) sakamakon matsayar da kungiyar tarayyar Afirka ta dauka na kin amincewa da mamayar Isra’ila a kan yankunan Falastinwa, hakan ya faranta ran Bangarori na Falastinu.

Bisa ga rahoton da kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar, sanarwar da shugabannin kasashen kungiyar tarayyar Afirka suka bayar a karshen zamansu karo na 34, hakan ya samu karbuwa daga bangaren gwamnatin Falastinawa, da kuma kungiyoyin gwagwarmaya a Falastinu.

A cikin bayanin bayan taro na zaman shugabannin kasashen kungiyar tarayyar Afirka, an bayyana cewa tarayyar Afirka tana nuna ciakken goyon bayanta ga al’ummar Falastinu, tare da bayyana mamayar yankunan Falastinawa da Isra’ila ke yi da cewa, hakan ya saba wa doka.

Ministan harkokin wajen gwamnatin Falastinu Rayad Almaliki yay aba da wannan matsaya ta kungiyar tarayyat Afirka dangane da batun Falastinu, tare da bayyana hakan a matsayin wani babban lamari wanda ya cancanci yabo.

Shi ma a nasa bangaren kakakin kungiyar Hamas Sami Zuhri ya bayyana cewa, suna jinjina wa kasashen Afirka, kan yadda suke nuna goyon bayansu ga al’ummar Falastinu, da kuma yin Allawadai da duk wani zaluncin Isra’ila a kansu.

Kasashen larabawa irin Masar da Aljeriya da kuma Tuniya da suke cikin kungiyar tarayyar Afirka, suna kara karfafa gwaiwar sauran kasashen kungiyar wajen mara baya ga lamarin Falastinawa.

 

3952822

 

captcha