IQNA

Tsohon Kaftin Din Manchester Ya Yabi Addinin Muslunci

22:59 - October 23, 2019
Lambar Labari: 3484184
Bangaren kasa da kasa, tsohon kaftin din kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ya yabi addinin muslunci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya ahbarat cewa,a  cikin wanta zantawa da ya yi da jaridar The News, Patrice Evra tsohon kaftin din kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ya yabi addinin muslunci tare da bayyana shi da cewa addini ne mai kyau.

Ya ce shi mabiyin addinin kirista a darikar Katolika, amma duk da haka ba zai rufe idonsa kan abubuwa masu kyauda suke tatatre da addinin musulunci ba.

Ya ce ya sha fuskantar matsala daga mahaifinsa a duk lokacin da yake yabon addinin muslunci, ya ce mahaifinsa shi ma kirista ne mabiyin darikar Katolika, amma ra’ayinsa ya sha banban da na mahaifinsa dangane da yadda suke kallon addinin muslucni.

Wannan dai ba shi ne karo farko Evra yake fitowa yana yabon addinin muslunci, domin kuwa koa  2017 a lokacin da aka yi ta sukar musulmi a Barcela da ke kasar Spain ya nuna fushinsa, inda ya fito yana kare musulmi da addinin muslunci.

A lokacin ya rika bayyana cewa, addinin musulunci ba addinin ta’addanci ba ne, addini ne sulhu da zaman lafiya wanda yake koyar da kyawawan dabiu, saboda hakan danganta musulmi da ta’addanci ba dalaci, ko da kuwa wasu musulmi sun yi haka ba da koyarwar addininsu suka yi aiki ba.

 

3851944

 

captcha