IQNA

Ayatollah Ozma Sayyid Ali Khamenei Ya Halarci Taron Arbaeen

23:48 - October 19, 2019
Lambar Labari: 3484168
Ayatollah Sayyid Ali Khamenei Jagoran juyin juya halin muslunci na kasar Iran ya halarci taron arbaeen a yau a Husainiyar Imam Khomeni.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a daidai lokacin da ake gudanar da tarukan arbaeen a yau a kasar Iraki, a kasar Iran ma an gudanar da wadannan taruka a yau, inda jagoran juyin juya halin muslunci ya Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya samu halarta.

Rahoton ya ce jagoran ya gabatar da dan takaikatcen jawabi dangane da wannan rana ta arbaeen na Imam Hussain (AS) inda ya bayyana cewa gudanar da tarukan arbaeen wata babbar dama ce ta yin tunatarwa dangane da abin da ya faru da zuriyar manzon Allah bayan cikar kwanaki arbaeen da kisan gillar da aka yi msuu.

Ya ce a duk lokacin da musulmi suka taru domin tunawa da wani lamari muhimmi da ya faru a cikin addinin muslucni, shi kansa wannan isar da babban sako ne na addini ga duniya.

Kamar yadda ya bayyana tunawa da Imam Hussain (AS) da cewa lamari wanda yake damfare da yin aiki da koyarwarsa, wadda ita ce koyarwar addinin muslucni wanda manzon Allah ya zo da shi kuma ya yi kira zuwa gare shi.

 

3850890

 

 

 

captcha