Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a jiya ne aka gudanar da zaman taro mai taken sunnar manzon Allah a kwalejin ilimin addini da ke birnin Alkahira na kasar Masar tare da halartar malamai da masana.
An gabatar da kasidua wajen taron, wadanda suke jaddada wajabcin yin koyi da sunnar manzon Allah da kuma yin riko da koyarwarsa a cikin dukkanin lamurran musulmi a matsayin mafita gare su a kan halin da suka samu kansu a ciki.
Taron ya gudana ne a karkashin jagorancin babban malamin cibiyar Azhar ta Masar Ahmad Tayyib, wanda malamai da dama daga cibiyar ta Azhar da wasu ciboyoyin addini na msara suka gabatar da jawabansu a wurin taron.