IQNA

Taro Kan Silima na Kasar Iran A Senegal

23:44 - June 24, 2018
Lambar Labari: 3482784
Bangaren kasa da kasa, taro kan silima na kasar Iran a kasar Senegal a cikin harsunan faransanci da kuma yarukan kasar.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a jiya ne aka gudanar da taro kan kan fina-finan kasar Iran da aka tarjama a cikin harsunan faransanci da kuma wasu yaruka na kasar Senegal a birnin.

A lokacin kaddamar da wadannan fina-finai an bayyana wannan aiki a matsayin mai matukar amfani, domin kuwa dukkanin fina-finan da aka gabatar suna magana ne a kan lamurra na tarihin muslunci.

Haka nan kuma wasu daga cikinsu suna bayani ne a kan lamura da suka shafi yanayin al’adu da zamantakewar jama’a.

Gwamnatin kasar Senegal ta yi na’am da wannan mataki wanda take kallonsa a matsayin wada zai kara habbaka alaka tsakanin al’ummomin kasashen biyu.

3725045

 

 

 

 

 

 

captcha