IQNA

Za A Samar Da Cibiyoyi 50 Na Hardar Kur’ani A Jordan

23:54 - June 22, 2018
Lambar Labari: 3482779
Bangaren kasa da kasa, ma’aikatar kula da harkokin addini a Jordan ta sanar da cewa ta amince da samar da cibiyoyi 50 na hardar kur’ani a ladin Kureh na kasar.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yada labarai na batra cewa, Haisam bani Arshid cewa, ma’aikatar kula da harkokin addini a Jordan ta sanar da cewa ta amince da samar da cibiyoyi 50 na hardar kur’ani a ladin Kureh domin yin amfani da wajen bayar da horo akn hardar kur’ani.

Ya kara da cewa dukaknin wuraren za a yi amfani da su a cikin wannan hutun bazara mai zuwa, kuma za a raba su kashi biyu domin ware wani cibiyoyi 25 ga kananan yara.

Daga cikin muhimman abubuwan da cibiyoyin za su mayar da hankali a kansu, baya ga koyar da harda, kuma za a rika koyar da wasu ilmomi na kur’ani kamar tajwidi da sauransu.

3724262

 

 

 

captcha