Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, wannan littafi an buga shi kuma ya fara shiga dakunan karatu a kasar.
Babbar manufar littafin dai ita ce bayani kan addinin kirista da kuma tasirinsa ta fuskar tarbiya, ta yadda littafin yake koyar da yin amfani da kyawawan dabiu da kuam nisantar munanan dabiu na shaidan.
Littafin ya kunsha shafuka 436, kuma yana samun karbuwa daga mabiya addinin kirista dukkanin fadin kasar ta Ghana, kamar yadda ya fara isa wasu kasashen yammacin nahiyar.