Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Sheikh Usman Nuhu Sharubutu babban limamin kasar Ghana mutum ne mai tasiri na addini da siyasa da kuma zamantakewa a kasar Ghana.
Malamin yana bayar da gagarumar gudunmawa a bangarori daban-daban na ci gaban musulmi a kasar Ghana, da kuma kare hakkokinsu na siyasa da addini.
Sheikh Usman Nuhu Sharubutu ya yi imanin cewa bai kamata a raba harkar shugabanci da addini ba, domin kuwa a duk lokacin da shugaba ya zama mai riko da addini, to zai girmama dan adam da kuma girmama sauran addinai.
A jiya ne aka karama malamin wanda ya cika shekaru 99 a duniya, tare da halartar manyan jami’ai da malamai da kuma wasu daga cikin jakadu na kasashen musulmi.