IQNA

Majalisar Malaman Aljeriya Maida Martani kan fatawar Kafurta Musulmi

16:27 - March 21, 2018
Lambar Labari: 3482497
Bangaren kasa da kasa, Majalisar malaman addinin muslunci a kasar Aljeriya ta mayar da martani kan fatawar da babban malamin 'yan salafiyya na kasar ya bayar, da ke kafirta wani bangaren musulmi.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a cikin bayanin da majalisar malaman addinin muslunci ta kasar Aljeriya ta fitar a jiya, ta bayyana cewa nauyi ne da ya rataya  a kan gwamnatin kasar da ta dauki matakan ladabtar da masu neman haifar da rashin jituwa tsakanin al'umma.

A cikin fatawar da babban malamin wahabiya 'yan saafiyya na kasar Aljeriya Muhammad Ali farkus ya bayar, ya bayyana mabiya darikun sufaye da da kuma 'yan siyasa da cewa kafurai ne, tare da bayyana cewa duk wani dan sunna da ya shiga siyasa ko ya mara baya ga wani dan siyasa ya fita daga musulunci.

Majalisar malaman addinin muslunci ta kasar Aljeriya ta bayyana wannan fatawa da cewa tana da matukar hadari, kuma ba fatawa ce da ta ginu a kan dalilai na hankali ba, balanata hujjoji na addinin musulunci.

Akasarin al'ummar kasar Aljeriya dai mabiya darikin sufaye ne, musamnan ma mabiya darikar Tijjaniya, wadda tafi samun karbuwa  a tsakanin al'ummomin kasar.

3701593

 

 

 

captcha