IQNA

An Bude Bangaren Kwana Na Mata A Cibiyar Ilimi Ta Kasar Ghana

22:52 - March 13, 2018
Lambar Labari: 3482472
Bangaren kasa da kasa, an bude bangaren kwana na makarantar hauza a kasar Ghana.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya hbarta cewa, ya nakalto daga bangaren hulda da jama'a na jami'ar musulunci ta kasar Ghana cewa, an bude bangaren kwana na mata a bangaren makarantar Hauza dake karkashin jami'ar.

Bangaren hauza ya kebanci ilimomin addinin muslucni ne da na shari'a da kuma kur'ani, wanda shi ma yake a karakshin tsari na jami'ar muslunci.

Nusratullah Maliki jakadan kasar Ira a kasar Ghana ya halarci bukin bude wannan wurin kwana na dalibai mata, tare da wasu daga cikin jami'an gwamnatin kasar Ghana.

Gwamnatin Iran ce ta gina jami'ar muslunci ta kasar Ghana, wadda manyan malaman jami'oi na kasar suke koyar da dukkanin bangarori na ilimomi, da suka hada da kimiyya da fasaha da dai sauran ilmomi da ake koyarwa a sauran jami'oin kasar.

Yanzu haka dai gwamnatin Ghana ta saka wannan jami'a  cikin jerin manyan jami'oi na kasar wadanda ake samun karatu da gogewa a dukkanin bangarori na ilmomi.

3699675

 

captcha