IQNA

Za A Kafa Wata Cibiyar Musulunci Domin Yaki Da Tsatsauran Ra'ayi A Kenya

22:50 - March 13, 2018
Lambar Labari: 3482471
Bangaren kasa da kasa, za a gina wata cibiyar yaki da tsatsauran ra'ayin addinin musucni a kasar Kenya.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa,shafin bc.co.uk ya habarta cewa, shugaban majalisar musulmin yankin Mombasa na kasar Kenya Abdulkadir Hidel ya bayyana cewa, za a kafa wata cibiyar musulunci da za ta yaki tsatsauran raayi.

Bayanin ya ci gaba da cewa, wannan cibiya za ta mayar da hankali ga ayyukan wayar da kai musamamn ga matasa, wadanda sune aka fi saurin rudarsu.

Kasar Kenya na daga cikin gabashin Afirka kuma mafi yawan mutanen kasar mabiya addinin kirista ne, amma musulmi suna da rinjayea  yankin Mombasa.

Kungiyoyin 'yan ta'adda musamman masu alaka da kungiyar Alshabab suna kaddamar da hare-hare a cikin kasar Kenya lamarin da yake bakanta sunan adinin muslunci a kasar.

3699186

 

 

 

 

 

 

 

 

 

captcha