IQNA

Bayani Kan Muslunci A Cibiyar Kiristanci Ta Lacras A Amurka

20:47 - October 21, 2017
Lambar Labari: 3482022
Bangaren kasa da kasa, wata cibiyar kiristanci a yankin Lacras a kasar Amurka ta gayyaci wasu daga cikin musulmin yankin domin yin bayani kan muslunci.

Kamafanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na WKBT cewa, cibiyar kiristanci a yankin Lacras a kasar Amurka ta gayyaci wasu daga cikin musulmin yankin domin yin bayani kan muslunci da kuma akidunsa.

Wannan shiri yana da alaka ne da yadda ake samun karuwar kyamar msuulmi a kasar wanda hakan ya sanya majami'oi suke daukar matakai na ganin sun jawo musulmi kusa domin rage kaifin adawa da kyamar da ake nuna musu.

Wasu daga cikin msuulmin yankin sun halarci wannan majami'a, inda suka gabatar da bayanai kan addinin msulunci tare da amsa tambayoyi kan zarge-zarge da dama da ake yi wa musulmi, musamman kan batun ta'addanci.

A cikin jawabin da musulmins uka bayar sun nuna wa dukkanin mahalarta wurin cewa, muslunci addini ne na zaman lafiya da fahimtar juna a tsakaninsa da sauaran, masu aikata ta'addanci da sunan muslunci basu wakiltar addinin muslunci da sauran musulmi, kamar yadda masu aikata ta'addanci daga cikin kiristocia Amurka da ma wasu yankuna, basa wakiltar addinin kirisa da sauran mabiya wannan addini.

3654905


captcha