Bayanin ya ci gaba da cewa, wannan dakin daukar shirye-shirye ya kunshi muhimman kayan aiki na zamani na daukar sauti mai inganci, ta yadda za a iya yin amfai da shi ta hanyoyi da dama.
Daga cikin hanyoyin da za a yi amfani da sautin da za a rika dauka a wannan wuri har da gidajen radio da kuma shafukan yada zumunta gami da shafuka na yanar gizo da suka danganci lamurran kur’ani mai tsarki.
Babbar manufar bude wannan studio da ita ce, kara inganta hanyoyin sauti na karatun kur’ani da ake dauka kuma ake watsa a kafofin yada labara kamar gidajen radio da talabijin da kuma shafukan sadarwa na zamani, ta yadda jama’a za su amfana da wannan aiki.