Kamfanin dilalncin labaran iqna ya ahbarat cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Manama Post cewa, wasu gunun masu adawa da kulla alaka da Isra'ila akasar Bahrain sun gudanar da gangamin nuna rashin amincewa da masarautar kasar na neman hada kai da yahudawan haramtacciyar kasar Isra'ila.
Bayanin ya ci gaba da cewa, babban dalilin da yasa wadannan mutane suka kirkiri wannan gangami shi ne nuna goyon baya ga al'ummar Palastinu da kuma gwagwarmayar da suke yi wajen neman hakkokinsu da yahudawa suka danne musu.
Dangane da yunkurin da masarautar mulkin kama karya ta Bahrain ke yin a neman dawo da alakar diflomasiyya a hukumance a kasar kuwa, gungun ya nuna cewa wanann cin
amanar al'ummar Palastinu da sauran al'ummomin larabawa da msuulmi ne.
Gwamnatin kama karya ta Bahrain dai tana da
kyakyawar alaka tare da gwamnatin yahudawan sahyuniya, kuma suna gudanar da
dukkanin harkokinsu a bayyane, duk da cewa a hukunamce babu alaka tsakaninsu,
amma kuma akwait a aikace.